Isa ga babban shafi

Najeriya: An kashe Mutane 201 a Filato cikin watanni 5

Akalla mutane 201 ne aka bada rahoton sun mutu a cikin watanni biyar a hare hare 27 da aka kai kananan hukumomi 7 na jihar Filato da ke Najeriya, kamar yadda jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa  a  kasar ta ruwaito.

Jihar Filato na fama da hare hare na 'yan ta'adda da kuma rikice rikicen kabilanci,inda a kwanan nan ne ma aka sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a karamar hukumar Mangu sakamakon rikicin kabilanci.
Jihar Filato na fama da hare hare na 'yan ta'adda da kuma rikice rikicen kabilanci,inda a kwanan nan ne ma aka sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a karamar hukumar Mangu sakamakon rikicin kabilanci. © KOLA SULAIMON/AFP
Talla

Kashe kashen sun auku ne daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa ranar 20 ga watan Yunin wannan shekarar da muke ciki.

Kanana hukumomin da wannan lamari  ya shafa sune: Riyom, Bokkos, Jos  ta Kudu, Jos ta Gabas, Barkin Ladi, Bassa da Mangu.

An tattara wadannan allkalumman ne daga kashe   kashen da  aka samu labarin su a jihar ne, kuma ana hasashen za a samu karuwar mamata.

Mazauna jihar da masu sharhi sun bayyana takaici a game da kashe kashen da ke aukuwa kwanan nan a jihar, inda suka ja hankali a kan makamancinsa a shekarar 2001, wanda aka kai shekaru sama da 10 ana yi, lamarin da ya lakume rayuka da kadarori da suka kai  bilyoyin nairori.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.