Gwamnatin Najeriya ta ce zata hukunta wadanda ke da hannu a kisan Filato
Gwamnatin Najeriya ta jajanta wa al’ummar yankin Bokkos da sauran yankunan da rikici ya shafa a jihar Plateau, inda alkalumma na baya-bayan nan ke cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sun doshi 200.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kunna - 03:01
A lokacin da ya jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnati ciki har da mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima, ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiyuwa domin gano wadanda suka aikata wannan kisa da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Muhammad Tasiu Zakari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu