Isa ga babban shafi

Tsohon gwamnan Yobe Abba Ibrahim ya rasu yana da shekaru 75 a duniya

Najeriya – Rahotanni daga Najeriya sun bayyana cewar Allah ya yiwa tsohon gwamnan Jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim rasuwa a kasar Saudi Arabiya yana da shekaru 75 a duniya.

Bukar Abba Ibrahim
Bukar Abba Ibrahim © Daily Trust
Talla

Tsohon gwamnan ya rasu ne sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da ita.

Ibrahim shine gwamnan farar hula na farko da ya jagoranci jihar Yobe a jamhuriya ta 3 a karkashin jam'iyyar SDP lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida shugaban gwamnatin sojin Najeriya.

Daga bisani Ibrahim ya sake zama gwamna a jamhuriya ta 4 wadda ke ci a karkashin tutar jam'iyyar ANPP inda ya kwashe shekaru 8 yana mulki.

Tsohon gwamnan na daga cikin jiga jigan 'yayan jam'iyyar ANPP da suka jagoranci rikidewar ta domin kafa jam'iyyar APC wadda ke mulkin Najeriya tun daga shekarar 2015.

Ibrahim ya taba zama sanata har sau 3 tsakanin shekarar 2007 zuwa 2019.

Tuni gwamnan jihar mai ci, Mai Mala Buni ya bayyana alhini rasuwar Abba Ibrahim da kuma mika sakon ta'aziya ga iyalansa da kuma al'ummar jihar Yobe baki daya.

A sakon ta'aziyar da Darakta Janar na gwamnan Mohammed Mamman ya rattabawa hannu, yace gwamnatin jihar na shirya jana'izar marigayin da kuma yadda jihar zata karrama shi saboda irin gudumawar da ya bayar wajen ci gaban ta.

Gwamna Buni wanda ya bayyana rasuwar a matsayin baban rashi ga jihar, ya bukaci al'umma da suka gabatar da addu'oi ga marigayin.

Buni yace lokacin mulkin marigayin a matsayin gwamna da kuma sanata, rayuwar mutanen jihar ta inganta.

Shima tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal ya mika sakon ta'aziyarsa dangane da rasuwar da kuma yabawa marigayin dangane da irin gudumawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Yobe da kuma Najeriya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.