Mutane sun mutu sakamakon ruftawar rami a Zamfara
Akalla mutane biyu ne suka mutu sannan wasu 10 suka jikkata a ranar Larabar da ta gabata sakamakon ruftawar wata mahakar zinari a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda wani jami'in hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar ya sanar.
Wallafawa ranar:
An gano gawarwakin mutanen biyu sannan mutane 10 na da raunuka daban-daban.
Babu wani bayani dangane da adadin masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da ake zaton sun mutu a wannan wuri biyo vayan wannan iftila’in ko suka makale a karkashin kasa," in ji Aliyu Kafindangi, manajan horar da jami’an hukumar kula da agajin gaggawa ta kasar Nema a arewa maso yammacin Najeriya.
A cewarsa, an ci gaba da aikin ceto a yau Asabar a kauyen Dan Kamfan, domin fito da gawarwakin masu hakar ma’adinai da suka makale a hadarin.
Kawo yanzu dai ba a san dalilan ruftawar wannan rami ,sai dai ana yawan samun hadurra a mahakar ma'adanai a yankin, gani ta yada mutane ke aiki ba bisa ka’ida ba kuma hanyoyin da ake amfani da sun bambanta da na zamani.
A bisa wasu dalilai na tsaro gwamnatin jihar Zamfara ta sake haramta ayyukan hakar ma'adanai a watan Satumban 2023. Jihar Zamfara na daya daga cikin yankunan kasar da ke fama da matsaloli da suka jibanci rashin tsaro .
A cikin 'yan shekarun nan a Najeriya, ayyukan hakar ma'adinai na janyo hadura ,al’amarin da ya as hukumomin sanar da daukar matakan sa ido a wannan sashe duk da cewa ana kyautata zaton kungiyoyi masu dauke da makamai na amfani da haka a wasu lokuta don afkawa ma’aikata da nufin yi musu fashi da makami.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu