Isa ga babban shafi

Yadda bangaren shari'a ya lalace a Najeriya - Olumide Akpata

Najeriya – Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya Olumide Akpata yace bangaren shari’ar kasar yayi lalacewar da yake da matukar wahala a samu tsayayyen alkali wanda zai gudanar da shari’a ta gaskiya ba tare da nuna son kai ba.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. 09/10/23
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. 09/10/23 © Bola Ahmed Tinubu twitter
Talla

Akpata wanda ke halartar taron kungiyar lauyoyi ta duniya a birnin Paris, yace ‘yan siyasa sun yiwa bangaren shari’a kamun kazar kuku, ta yadda suke sanya ‘yayansu ko abokansu ko matansu ko kuma ‘yan uwansu domin biyan bukatar kansu.

Tsohon shugaban yace samun mutumin kirki da zai tsallake dukkanin shingen da wadannan ‘yan siyasa ke sanyawa domin gudanar da alkalanci ba abu ne mai sauki ba, sai dai dace kawai.

Nigerian Supereme Court
Nigerian Supereme Court nigerianpilot.com

Akpata yace lokacin da yake shugabancin lauyoyin Najeriya baki daya, ya gano cewar ‘yan siyasa da gangan na kokarin dankwafe aikin shari’a, wanda hakan zai yiwa bangaren illa musamman ga wadanda ke neman hakkin su.

Jami’in yace daukar wannan mataki a wurin su ba wai kuskure bane, sai dai wani shiri na musamman domin ganin sun aiwatar da abinda suke so a koda yaushe, musamman ganin irin mutanen dake zama alkalai a sassan kasar.

Hanyoyin da ake bi wajen zabo mutanen dake zama alkalai a Najeriya ya lalace, abinda ya sa lauyoyi da dama ke bukatar ayi masa garambawul.

Akpata yace yanzu haka akwai ‘yayan tsoffin alkalai da wadanda ba suyi ritaya ba, da kuma matan su ‘yan siyasa da suka mamaye kujerun alkalanci a kotuna, abinda ke zubar da kimar bangaren shari’a a idan al’umma.

Tsohon shugaban ya zargi ‘yan siyasa, musamman gwamnoni da mayar da alkalai su zama maroka wajen hana su hakkokinsu da kuma kudaden da doka tace a basu, kamar motocin hawa da gidaje domin biyan bukatun kansu.

‘Yan Najeriya sun dade suna korafi a kan yadda bangaren shari’ar da talakawa da kuma marasa karfi suka dogara da shi ke neman zama wani dandali na rashin adalci wajen bi musu hakkokin su.

Ko bangaren siyasa, wasu jama’ar kasdar da dama na bayyana damuwa a kan yadda kotunan ke karbe nasarorin da wasu ‘yan siyasa suka samu na zabe, suna mikawa wasu, ba tare da la’akari da abinda jama’a suka zaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.