Isa ga babban shafi

Najeriya: Haɗarin kwale-kwale ya hallaka mutane sama da 30 a Taraba

Akalla mutane 32 ne, da suka hada da kananan yara 20 da iyaye 12 suka rasa rayukansu, sakamakon wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a karamar hukumar Ibbi ta jihar Taraba.

Wasu kwale-kwale a kan kogi
Wasu kwale-kwale a kan kogi AFP PHOTO / RIJASOLO
Talla

Bayanai sun ce, kwale-kwalen na dauke da masunta 50 ne da suka fito daga yankin Ibbi, kafin ya nutse a yankin Zabi da ya hada jihar ta Taraba da Benue. 

Wani dan mazauni Ibbi mai suna Malam Ibrahim Ibbi ya bayyana cewa yara 20 da iyaye 12 ne suka mutu a hatsarin.

Yadda hadarin ya auku

Alhaji Jidda Sulaiman, shugaban sashen kula da zirga-zirgar sufurin ruwa ta jihar Taraba, ya tabbatar RFI Hausa yadda suka samu labarin lamarin da kuma abin suke ganin ke haifar da hatsarin.

A halin da ake ciki, Gwamna Agbu Kefas, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, wanda ke zuwa kwanaki kadan bayan makamancin hadari ya auku Karim Lamido.

Ya jajantawa al'ummar Ibbi da addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

Sakon gwamnan jihar

Kefas, a wani sako da ya aike ta hannun babban mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa na zamani, Mista Emmanuel Bello, ya ce lamarin abin takaici ne samun wannan iftil’in biyo bayan kifewar wani kwale-kwale a Karim Lamido wanda ya jefa jihar cikin alhini.

Ya ce tuni gwamnati ta tashi tsaye wajen gudanar da bincike domin gano musabbabin yawaitan hatsarin kwale-kwale a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.