Isa ga babban shafi

'Yan mata 15 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Sokoto

Akalla 'yan mata 15 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hatsarin kwale-kwale a kauyen Dandeji da ke Karamar Hukumar Shagari a Jihar Sokoto ta Najeriya a kan hanyarsu ta zuwa daji domin neman itacen girki a safiyar Talatar nan.

Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a wasu yankuna na arewacin Najeriya.
Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a wasu yankuna na arewacin Najeriya. AFP/François Xavier Marit
Talla

Wadanda suka shaida lamarin sun ce, sama da mata 40 ne ke cikin kwale-kwalen lokacin da hatsarin ya auku.

Daya daga cikin mazauna yankin Muhammad Ibrahim ya ce, tuni aka gano gawarwaki 15 na 'yan matan kuma har yanzu masu iyo na ci gaba da neman sauran matan da lamarin ya rutsa da su.

Tuni dai aka yi wa gawarwakin sutura domin gudanar da jana'izarsu kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.