MDD za ta inganta kiwon lafiya a jihar Yobe ta Najeriya
Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kula da lafiya a jihar Yobe ta Najeriya wanda ake sa ran zai samar da ingantaciyar lafiya ga mutane miliyan uku a jihar, yawancinsu wadanda matsalar ta Boko Haram ta shafa.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:06
Matsalar tsaro ta yi matukar illa ga bangaren kiwon lafiya a jihar ta Yobe, inda ya sa gwamnatin tare da Majalisar Dinkin Duniya suka kudiri aniyar farfado da bangaren na kiwon lafiya don saukaka wa al'umma wahalar da suke sha a yanzu.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Bilyaminu Yusuf
Majalisar Dinkin Duniyar ta yaba wa gwamnatin jihar ta Yobe kan yadda ta samar da wasu cibiyoyi na kula da lafiyar kananan yara da mata da ke rasa rayukansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu