Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da laluben mutane fiye da 70 da suka nutse a kogin Benue

Bayanai daga jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce ana ci gaba da laluben mutane sama da 70 da suka bace, bayan kifewar da wani jirgin ruwa yayi dauke da fasinjoji fiye da 100 a kogin Benue.

Wasu masu aikin ceto yayin kokari ciro wadanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Taraba.
Wasu masu aikin ceto yayin kokari ciro wadanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Taraba. © Ahmad Alhassan/RFI Hausa
Talla

Jirgin ruwan da ya yi hatsari a ranar Asabar din da ta gabata, na dauke ne da fasinjooji ‘yan kasuwa da ke kan hanyar komawa gida bayan kammala hada-hadar cinikayya a kasuwar kifi da ke garin Ardo Kola.

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AP, Ladan  Ayuba, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ya ce mutane 14 aka samu nasarar cetowa da ransu, yayin da kuma aka ciro gawarwaki 17, ragowar 73 da suka bace kuma ake ci gaba da lalubensu.

Bincike dai na ci gaba da gudana don gano abinda ya janyo aukuwar hatsarin, wanda ake fargabar akwai yiwuwar a shafe kwanaki ana aikin laluben mutanen da suka bace bayan nutsewar da jirgin ruwan nasu yayi.

Yayin bayyana alhininsa kan hatsarin cikin wata sanarwa, gwamnan Taraba Agbu Kefas ya ba da umarnin tilasta wa fasinjoji sanya rigar kariya daga nutsewa a ruwa da aka fi sani da ‘Life Jacket’ a turance.

Gwamnan ya kara da cewar: Kamata yayi sufurin jiragen ruwa ya zame mana hanyar bunkasa tattalin arziki, amma ba silar salwantar rayuka ba.

Karo na uku kenan da hatsarin jirgin ruwa ke rutsawa da fasinjoji fiye da 100 a sassan arewacin Najeriya, lamarin da ake dangantawa da matsalar daukar mutane fiye da kima da ake lafta wa jiragen ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.