Isa ga babban shafi

Mutane dubu 1 da 188 sun kamu da cutar kwalara a jihar Zamfara - Gwamnati

Alkaluman da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar na nuna yadda aka tabbatar da kamuwar akalla mutane dubu 1 da 188 da cutar kwalara a sassan kananan hukumomin jihar 14, matsalar da masana ke alakantawa da rashin tsaftataccen ruwan sha.

Ana dai ganin tsanantar cutar kwalara a sassa daban-daban na nahiyar Afrika.
Ana dai ganin tsanantar cutar kwalara a sassa daban-daban na nahiyar Afrika. REUTERS/Andres Martinez Casares
Talla

Alkaluman wanda ma’aikatar lafiya jihar ta bakin kwamishina Aishatu Anka ta sanar sun nuna cewa an samu wannan adadi na masu fama da cutar ne daga watan Disamban bara zuwa yanzu.

A cewar kwamishinar wadda ke bayar da alkaluman yayin isar da wasu kayakin kula da masu cutar ta kwalara a cibiyar kula da su da ke birnin Gusar, ta ce cikin wannan alkaluma akwai mutane 40 da cutar ta kashe cikin watanni 10 da suka gabata.

Kwamishinar ta ce duk da yadda aka yi nasarar yakar cutar a kananan hukumomin Gusau da Anka da Bakura da kuma Bukkuyum, amma ana ci gaba da ganin wadanda suka kamu da ita a sauran sassan jihar.

Wannan alkaluma na masu fama da cutar kwlaara dai na zuwa ne a dai dai lokacin da cutar mashakon Diphtheria ta bulla a jihar ta Zamfara inda zuwa yanzu aka tabbatar da mutane 50 da suka harbu da ita ciki har da 2 da cutar ta kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.