Isa ga babban shafi

Gwamnatin Buhari ta gaza, yanzu rayuwar nadama ya ke - Dalung

Tsohon ministan ci gaban matasa da wasanni a Najeriya Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari na nadama kan yadda makusantansa suka bata masa suna a lokacin shugabancinsa.

Tsohon ministan wasanni na Najeriya Barista Solomon Dalung.
Tsohon ministan wasanni na Najeriya Barista Solomon Dalung. RFI/Bashir
Talla

Dalung da ya yi aiki a karkashin gwamnatin Buhari, ya ce gwamnatin ta gaza wajen cika alkawuran da ta daukarwa ‘yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe na shekarar 2015.

A wata zantawa da gidan Radio Trust, tsohon ministan ya ce a matsayinsa na wanda suka kafa jam’iyar APC ya zame masa wajibi ya fadi gaskiyar abinda ke faruwa.

Ya ce a lokacin yakin neman zabe, sun yi wa ‘yan Najeriya alkawarin samar da tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar da kuma yakar cin hanci da rashawa, amma sai dai ya ce sun gaza cika alkawuran da suka dauka.

Dalung ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya, wanda ya kuma yarda da mutanen da ke tare dashi, duk da cewa su ne suka bata masa suna.

Tsohon ministan ya ce gwamnatin jam’iyar APC daga tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 ta samu nasarori, domin allamuran tsaro a lokacin ba su tabar-bare kamar yanzu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.