Isa ga babban shafi

Buhari ya gaza, amma bama goyon bayan a tsige shi - Premium Times

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta bayyana cewar rashin iya shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka wajen baiwa 'yan ta’adda damar cin karen su babu babbaka a sassan kasar, abinda ke kaiga rasa rayuka da asarar dukiyoyi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

Sharhin da Jaridar ta gabatar yau, ya bayyana cewar wasu manya manyan hare hare guda 2 da kungiyar ISWAP ta kai ya tabbatar da matsayin ta na barazanar sace shugaban kasar domin yin garkuwa da shi.

Jaridar tace a watan Maris, wani reshe na kungiyar da ya mamaye dajin jihohin Kaduna zuwa Neja, ya kai hari akan jirgin dake safara tsakanin Abuja zuwa Kaduna, inda ya kashe wasu daga cikin fasinjojin da kuma sace mutane 62 daga cikin su, inda suka gindaya diyyar naira miliyan 100 akan kowanne mutum daga cikin mutane 35 da suka sake.

Hari kan jirgin kasa ya haifar da shakku kan shugabancinmu - Gwamnoni

Premium Times tace bayan kwashe watanni ba tare da daukar wani mataki ba, 'yan uwa da iyalan fasinjojin da akayi garkuwa da su, sun bazama wajen sayar da kadarorin su domin tara kudin fansa da aka bukaci su biya, yayin da jami’an gwamnati suka mayar da hankali wajen nuna yatsa a tsakanin su.

 

Jaridar tace a watan Yuli, kungiyar ISWAP tare da taimakon Ansaru wadda ta balle daga boko haram dake da sansani a jihohin Kaduna da Kogi ta kai wani kazamin hari akan gidan yarin Kuje dake Abuja, inda ta kashe jami’in tsaro guda, ta kuma kubutar da mutane 879, cikin su harda ‘yan boko haram 64.

Mayakan da ake zargin na jihadi ne, sun balle gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin tarayyar najeriya tare da sakin fursunoni
Mayakan da ake zargin na jihadi ne, sun balle gidan yarin Kuje da ke Abuja babban birnin tarayyar najeriya tare da sakin fursunoni © Afolabi Sotunde, Reuters

Harin na Kuje ya gamu da mummunar martani daga 'yan Najeriya wadanda suka fusata da rawar da gwamnati ke takawa, yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kai ziyarar gani da ido, inda yayi tambayoyi ga hukumomin gidan yarin da kuma barazanar daukar mataki.

Tashe-tashen hankula a Najeriya

Jaridar tace jim kadan bayan harin gidan yarin, 'yan bindigar sun kai hari akan tawagar motocin shugaban kasar dake kan hanyar zuwa Daura, wato mahaifarsa inda suka yi musayar wuta, yayin da wasu kuma suka yiwa sojojin dake rundunar tsaron dake kare shugaban kasa kwantan bauna a Abuja, inda suka kashe wasu daga cikin su.

Premium Times tace bayan wadannan hare hare, sai 'yan bindigar suka saki bidiyon dake dauke da sauran fasinjojin jirgin kasan da suka yi garkuwa da su, inda aka nuna su suna musu bulala, yayin da shugaban su da yace yana daya daga cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin Kuje, yayi barazanar kama shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai. © Daily Trust

Jaridar tace bayan wadannan hare hare da kuma wasu tari a sassan Najeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya dace ya yiwa 'yan kasa bayani na musamman akan yadda ya nada shugabannin hukumomin tsaron yadda yake so ba tare da la’akari da kabila ko addini ko shiya ba saboda son kai, yayin da ya mallaki majalisar dokoki wadda take taka rawar da yake so a kowanne lokaci wajen biya masa bukata, kana a bangare daya bangaren shari’a ya zama wanda ya bada kai wajen goyan bayan sa.

Premium Times ta bada shawara akan jerin matakan da gwamnati ya dace ta dauka domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya a yau da suka hada da bunkasa rayuwar jama’ar kasa da kuma gina su akan tafarkin tsaro da rungumar zuba jari a bangaron tsaro tun daga matakan karkara da gabatar da shirin noma da bunkasa samar da ruwan sha na gaskiya tare da harkar hakar ma’adinai, sai kuma samar da gurabun ayyukan yi ga dimbin matasan da ake da su a kasa.

Jaridar tace aiwatar da wadannan tare da inganta shirin samar da zaman lafiya na karkara zasu taimaka gaya, maimakon zuba makudan kudade da suna aikin samar da tsaro a aljihun Janar Janar na soji da 'yan kwangilar dake aikin sayen makamai.

Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar gawamnatin kasar dake Abuja  yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar gawamnatin kasar dake Abuja yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari. © Presidency of Nigeria

Jaridar tace sauraron shawarwari daga kowanne bangaren al’umma zai taimaka a wajen lalubo hanyoyin fitar da Najeriya daga halin kuncin da ta samu kan ta, amma abin takaici, yana da wahala shugaban kasa ya saurari wadannan shawarwari, abinda ya sa 'yan majalisa daga bangaren Jam’iyyar PDP suka bukaci tsige shi a makon jiya,

Premium Times tace bata goyan bayan tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, duk da cewar ana amfani da shirin wajen ladabtar da yan siyasar da suka gaza, amma kuma yunkurin haka zai zama bata lokaci da kawar da hankali akan abinda ba zai yiwu ba, musamman ganin cewar saura watanni 8 a zabi sabon shugaban kasa, kuma wannan itace hanyar da ta fi dacewa ga 'yan Najeriya su zabarwa kan su shugaban da suke so.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.