Isa ga babban shafi

Buhari ne mafi munin shugaba da Najeriya ta gani a tarihi- Hanga

Zababben sanatan da zai wakilci Kano ta tsakiya a Majalisar dattawan Najeriya Rufa'i Hanga, ya bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mafi muni da kasar ta taba gani a tarihi. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

A lokacin wata ganawa da ya yi da kafar Talabijin ta Trust TV, Rufa'i Hanga da ya yi shura wajen tallata siyasar shugaban Muhammadu Buhari a jihar Kano tsawon shekaru, ya ce shugaban ya gaza kuma bashi da nagartar jagoranci. 

A cewar zababben sanatan na Kano ta tsakiya, Buhari bai can-canci a rinka kiran sa da sunan ''Mai Gasiya ba'', ganin yadda ya ke kewaye da mutanen da ke fuskantar tuhuma a wajen hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriyar EFCC. 

Sanata Hanga ya ce babu wani shugaba da zai gudanar da salon mulkin Buhari ya kuma yi ikirarin shi ya fi kowane shugaba gudanar da aiki a Najeriya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.