Isa ga babban shafi

'Yan sanda sun kame Naira Marley kan zargin hannu a mutuwar MohBad

Rahotanni daga jihar Lagos ta kudancin Najeriya, sun tabbatar da kame fitaccen mawakin kasar Azeez Fashola da aka fi sani da Naira Marley dangane da zargin hannu a mutuwar guda cikin yaransa kuma abokin aikinsa Ilerioluwa Aloba da aka fi sani da MohBad.

Wata zanga-zangar bukatar bincike kan mutuwar MohBad.
Wata zanga-zangar bukatar bincike kan mutuwar MohBad. AP - Sunday Alamba
Talla

Kamen na Naira Marley da ke zuwa jim kadan bayan isar shi Najeriya bayan dogon hutu a ketare, na zuwa ne bayan mabanbantan zanga-zangar da 'yan kasar suka rika yi don daukar mataki kan wadanda ke da hannu a mutuwar matashin mawakin MohBad.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kamen Naira Marley a daren jiya Talata, wanda ya ce zai amsa tambayoyi game da zargin.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafin X da aka fi sani da Twitter, Hundeyin ya ce rundunar ‘yan sandan za ta ci gaba da tsare Naira Marley wanda za a fadada bincike akansa bayan amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na hannu a mutuwar MohBad.

Bayan mutuwar MohBad a ranar 12 ga watan da ya gabata na Satumba da kuma birne shi a washegarin ranar ne, korafe-korafe suka tsananta game da hannun Naira Marley da wasu mawaka ciki har da Sam Larry game da yadda suka tsawwala rayuwa ga mamacin har ta kai ga rasa rayuwarsa.

Tun gabanin kamen na shi a jiya Talata, Marley yayin wata zantawarsa da Reno Omokri ya bayyana cewa a shirye ya ke ya mika kansa ga jami’an tsaro don bincikensa game da zargin mutuwar ta MohBad haka zalika don samun kariya daga fusatattun matasa.

A cewar Naira Marley baya Najeriya tun ranar 31 ga watan Agusta kuma shi kansa a shafukan sada zumunta ya ci karo da labarin mutuwar MohBad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.