Isa ga babban shafi

Ganduje na shirin zama shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya

Rahotanni na cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai rike shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na rikon kwarya.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganguje © This Day
Talla

Ganduje, mai shekaru 73, a ranar Laraba ne ya ziyarci fadar shugaban kasar da ke Abuja, inda ya gana da Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni uku ‘yan jam’iyyar ta APC.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito bayanai na cewa, za a nada tsohon gwamnan a matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ta kasa, har zuwa lokacin da za a gudanar da babban taron jam’iyyar a shekara mai zuwa.

A ranar Lahadi ne, tsohon shugaban Jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya mika takardar ajiye aiki, biyo bayan zargin bita da kullin kawar da shi. Shima babban sakataren jam’iyyar na kasa, Iyiola Omisore ya mika takardar ajiye aiki.

Ganduje zai karbi ragamar mulki daga hannun Sanata Abubakar Kyari wanda aka nada a matsayin shugaban riko na kasa ranar Litinin. Kyari, wanda ya fito daga jihar Borno, shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga shiyyar Arewa.

An ruwaito cewa shugaba Tinubu ya dawo daga taron kungiyar tarayyar Afrika a kasar Kenya a ranar Litinin din da ta gabata, inda ya nuna sha’awarsa ta mayar da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar.

Don haka ne aka tuntubi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin, domin janyo hankalin takwarorinsa da sauran masu ruwa da tsaki.

Uzodinma ya gana da Ganduje a ranar Talata, kuma a ranar Laraba sun gana da shugaba Tinubu tare da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun.

 

A wajen taron, wata majiya ta fadar shugaban kasar ta ce an kammala tattaunawar da zaben Ganduje. Bayan haka shugaban kasa da gwamnoni uku da Ganduje sun gana da mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima.

 

Wata majiya ta ce, “A ranar Litinin ne batun mayar da Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar ya fara ne lokacin da shugaban kungiyar gwamnoni ta PGF ya gana da shi a Abuja. Uzodinma ya shaidawa tsohon gwamnan jihar Kanon kudirin shugaban kasa na nada shi shugaban jam’iyyar na rikon kwarya.”

 

Ya ce an kammala maganar ne a jiya lokacin da shugaban kasa ya gana da Ganduje tare da gwamnonin uku.

 

“Daga dukkan alamu, an rufe batun da cewa Ganduje ne zai karbi shugabancin jam’iyyar APC. Majiyar ta kara da cewa za a fara bayyana shi a matsayin shugaban riko na kasa kafin babban taron jam’iyyar.

 

Da wannan ne, kujerun shugabancin jam’iyyar sun tashi daga shiyyar Arewa ta tsakiya inda Sanata Adamu ya fito, wanda ficewar sa ya sa jiga-jigan jam’iyyar a shiyyar sa fara neman mafita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.