Isa ga babban shafi

Mutane 20 sun makale a cikin wani bene da ya rushe a Abuja

Rahotanni daga Najeriya na cewa wani gini mai hawa hudu ya rushe a yankin Life camp da ke birnin tarayyar kasar Abuja. 

Mutane 20 sun makale bayan da wani bene da ake kan aikin sa ya rushe a Abuja.
Mutane 20 sun makale bayan da wani bene da ake kan aikin sa ya rushe a Abuja. © PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Ganau sun shaidawa manema labarai cewa ginin wanda ake kan aikin sa yanzu haka ya fado ne da yammacin jiya Litini, kuma ana fargabar ya danne mutane fiye da 20. 

Kafofin yada labaran cikin gidan kasar sun ruwaito cewa dama inda ake ginin ya gamu da ibtila’in ambaliyar ruwa a makon da ya gaba, amma bayan janyewar Ruwan ma’aikatan suka koma don ci gaba da aiki. 

Tun lokacin faruwar lamarin ne kuma jami’an hukumar bada agajin gaggawa da na kashe gobara suka isa wajen don kokarin zakulo mutanen da suka makale a karkashin baraguzan ginin da ya fado. 

A cewar jaridar Leadership da ake wallafawa a kasar, karfe 8 saura na daren litinin din an samu nasarar ceto mutane 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.