Isa ga babban shafi
NAJERIYA-HADARI

Mutane 15 suka mutu a hadarin benen Lagos - NEMA

Yau an ci gaba da gudanar da aikin agaji a inda wani bene mai hawa 21 ya rufka akan ma’aikatan dake aikin ginin a birnin Lagos dake Najeriya, inda aka samu rasa rayuka, yayin da kuma akayi nasarar zakulo wasu mutane biyu da ran su.

Yadda ake ci gaba da aikin ceto a wurin da bene mai hawa 21 ya fadi a Lagos
Yadda ake ci gaba da aikin ceto a wurin da bene mai hawa 21 ya fadi a Lagos © RFI Hausa
Talla

Hukumomin agaji da na tsaro sun mamaye ginin da aka samu hadarin tare da masu aikin agajin dake amfani da manyan motocin tono domin zakulo wadanda ginin ya fada akan su.

Shugabar kungiyar agaji ta Red Cross a Jihar Lagos Adebola Kolawole ta tabbatarwa RFI Hausa  nasarar ceto mutane biyu da ran su ayau.

Abinda ya rage daga benen da ya fadi a birnin Lagos
Abinda ya rage daga benen da ya fadi a birnin Lagos Benson Ibeabuchi AFP

Wani dan kwangila kuma Abashe Maisule yace, yaran sa guda 4 ke aiki a wurin lokacin da aka samu hadarin, yayin da biyu daga cikin su sun yi nasarar tsallake rijiya da baya, sauran kuma babu duriyar su.

Jami’in yada labaran Hukumar agajin gaggawa Ibrahim Farinloye ya bayyana cewar ya zuwa yau an samu gawarwakin mutane 15, yayin da jami’an su tare da abokan aikin su na jihar Lagos ke ci gaba da gudanar da aiki a wurin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci hukumomin da su gaggauta ceto wadanda hadarin ya ritsa da su a sanarwar da ya rabawa manema labarai, yayin da ya jajantawa ‘Yan uwan wadanda ke ciki.

Iyalai da ‘Yan uwan ma’aikatan dake cikin ginin sun mamaye kofar shiga wurin aikin ceton domin ganin ko zasu samu labarin su daga masu aikin ceton.

Tuni gwamnan lagos Babajide Sanwo-Olu ya bada umurnin gudanar da bincike akan hadarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.