Isa ga babban shafi

Ana fargabar mutuwar tarin mutane bayan ruftawar bene mai hawa 20 a Lagos

Rahotanni daga jihar Lagos a tarayyar Najeriya sun bayyana yadda wani bene mai hawa 21 da ake tsaka da aikin gininsa ya rufto inda ake fargabar mutuwar tarin jama'a galibinsu ma'aikatan da ke tsaka da aiki.

Faduwar wani gini a jihar Lagos.
Faduwar wani gini a jihar Lagos. © RFI Hausa
Talla

Lamarin dai ya faru ne a unguwar Ikoyi da ke karamar hukumar Eti Osa, inda shaidun gani da ido suka tabbatar da cewa mutanen da baraguzan ginin ya rufe da su a ciki za su iya haura mutum 100 galibinsu 'yan aikin kankare.

Har zuwa wasu sa'o'i bayan faruwar lamarin dai babu jami'an agajin da suka iya kai dauki wajen da lamarin ya afku.

Wasu da ke wajen da ginin ya ruguzo a Ikoyi ta jihar Lagos.
Wasu da ke wajen da ginin ya ruguzo a Ikoyi ta jihar Lagos. © RFI Hausa

Haka zalika babu cikakken bayani kan yawan mutanen da suka rasa ransu ko kuma suka jikkata a iftila'in.

Wasu bayanai dai sun ce ginin mallakin wani kusa ne a gwamnatin Najeriya.

Ruftawar gine-gine ana tsaka da aikinsu ba sabon abu ba ne a Lagos bayanda ake ci gaba da samun karuwar masu gine-gine marasa inganci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.