Isa ga babban shafi
Najeriya-Lagos

Ruftawar bene ta kashe Masallata a Lagos

Rahotanni daga jihar Lagos ta Najeriya sun ce, wani ginin bene ya rufta kan jama'a da suka hada da wasu leburori da ke kan gudanar da salla a unguwar Obalende, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla takwas.

Wurin da ibtila'in ya faru
Wurin da ibtila'in ya faru Punch
Talla

Hukumar Agajin Gaggawa ta Lagos ta bakin kakakinta Nosa Okunbor ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa, an yi nasarar ceto mutane 20 da ransu bayan baraguzai sun danne su.

Sai dai 10 daga cikinsu sun samu munanan raunuka, yayin da aka kai su babban asibitin tsibirin Lagos domin kula da lafiyarsu.

Babu cikakken bayani game da musabbabin aukuwar ibtila'in amma bayanai sun tabbatar cewa tun da jimawa, gwamnati ta dakatar da aikin  ginin mai hawa uku saboda rashin ingancinsa, amma masu ginin suka yi watsi da umarnin.

Wata majiya ta ce, masu ginin sun yi amfani da shinge domin kange ginin, abin da ya ba su damar ci gaba da aikinsu ba tare da sanin hukuma ba.

Mutanen da ibtila'in ya cika da su leburori ne kuma akasarinsu Hausawa ne kamar yadda wata majiya ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.