Isa ga babban shafi

Buhari ya sanyawa tashoshin jiragen sama sunan fitattun ‘yan kasar

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanyawa tashoshin jiragen saman kasar mallakar gwamnatin tarayya sunayen wasu fitattun jama’ar kasar da suka bada gudumawa a fannoni daban daban. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Sanarwar da kakakin ma’aikatar sufurin jiragen sama Odutayo Oluyesi ya rabawa manema labarai, ta bayyana cewa Buhari ya amince da sanya sunayen ne a ranar juma’ar da ta gabata. 

Daga cikin wadanda aka nada sunayen su akwai Sheikh Usman Danfodio da Obafemi Awolowo da janar hassan Usman Katsina da Janar Tunde Idiagbon da JS Tarka. 

Wasu daga cikin tashoshin da nadin sunan ya shafa sun hada da na Akure da Dutse da Binin da Gombe da Maiduguri da Yola da Akure da kuma Kaduna. 

Ga jerin tashoshin da kuma sunayen da aka rada musu. 

Ibadan – Samuel Ladoke Akintola 

Ilorin – Janar Tunde Abdullahi Idiagbon 

Kaduna – Janar Hassan Usman Katsina 

Maiduguri – Muhammadu Buhari 

Makurdi – Joseph Sarwuan Tarka 

Minna – Abubakar Imam 

Nasarawa – Sheikh Usman Danfodio 

Asuba – Alfred Diete Spiff  

Fatakwal – Obafemi Jeremiah Awolowo 

Yola – Lamido Aliyu Mustapha 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.