Isa ga babban shafi

Buhari na shirin ciyo bashin Dala miliyan 800

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci Majalisar Dattawan kasar da ta amince masa ciyo bashin Dala miliyan 800.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS - GONZALO FUENTES
Talla

Shugaba Buhari ya gabatar da bukatar ce a cikin wata wasika da ya shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta a wani zama da mambobin majalisar suka yi a jiya Talata.

A cikin wasikar, shugaba Buhari ya yi bayanin cewa, za a yi amfani da bashin ne domin fadada wani shiri na samar da walwalar jama'ar musamman talakawa da gajiyayyu a fadin kasar.

Shugaba Buhari ya ce, za a ciyo sabon bashin ne daga Bankin Duniya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ke shirin mika mulki a ranar 29 ga wannan wata na Mayu ga magajinsa, Bola Ahmed Tinubu da ya lashe zaben shugaban kasa a cikin watan Fabairun da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.