Isa ga babban shafi

'Yan Najeriya na bayyana damuwa akan nade naden da Buhari keyi

'Yan Najeriya na bayyana damuwar su akan yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma wasu gwamnonin kasar ke ci gaba da nada mukamai da kuma bayar da kwangiloli a daidai lokacin da suke gab da sauka daga karagar mulki. 

Shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari sanye da kayan sojoji a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammmadu Buhari sanye da kayan sojoji a filin taro na Eagle Square da ke Abuja. © Nigerian Army
Talla

Yayin da wasu mutane ke kallon matakin a matsayin wani tarko da gwamnatin ke ‘danawa wadanda zasu gaje su, zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamnoni masu jiran gado, musamman wadanda suka fito jam’iyya guda da wadanda zasu gada, sun ki cewa uffan a bainar jama’a dangane da wadannan matakan da ake dauka. 

Rahotanni daga matakin tarayya zuwa na jihohi na nuna yadda shugaban kasa Buhari ke ci gaba da nade nade da kuma amincewa da sabbin kwangiloli na miliyoyin nairori, yayin da suma gwamnonin jihohi ke bin wannan mataki, wanda ke samun goyan baya ko amincewar majalisar kasa da ta jihohin. 

Daga cikin irin wadannan bukatu harda amincewar ciwo bashin dala miliyan 800 daga Bankin Duniya da majalisar kasa tayi domin rabawa talakawa a matsayin rage radadin cire tallafin man da gwamnati ta dakatar da aiwatarwa da kuma gabatar da bukatar biyan dala miliyan 556 da fam miliyan 98 da naira miliyan 226 a matsayin basussukan shari’ar da ake bin gwamnatin tarayya. 

A jihar Taraba, an ruwaito gwamna Darius Ishaku ya samu amincewar majalisar dokoki domin sayawa kansa da mataimakin sa motocin naira biliyan 2, bayan ya kaddamar da wasu jerin gidaje 500 da ba’a kammala aikin gina su ba. 

Takwaransa na jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya gabatar da kasafin kudin naira biliyan 71 wa majalisar dokoki kwanaki 14 kafin karewar wa’adin mulkinsa, yayin da David Umahi na jihar Ebonyi ya bukaci bashin naira biliyan 33 domin abinda ya kira kammala wasu ayyuka. 

Shi kuwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ana zarginsa ne da yin tarin nade naden manyan jami’an gwamnati wadanda ake ganin zasu kara yawan kudaden da sabuwar gwamnati zata kashe wajen biyansu hakkokin su. 

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa shima gwamnan Katsina Aminu Bello Masari wasu nade nade yayi wadanda ake ganin sun dace ya barwa gwamnati mai zuwa. 

Sai dai masana harkar shari’a sun bayyana cewar wadannan zababbun shugabanni na da hurumin gudanar da ayyukansu har zuwa safiyar ranar 29 ga watan Mayu da zasu mika mulki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.