Najeriya: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 16 a Zamfara
Rahotanni daga jihar Zamfara dake Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 16 a wasu hare-haren da suka kai sassan jihar.
Wallafawa ranar:
Talla
Maharan sun kai farmaki ne kan kauyukan Birnin Magaji da Mazauda da Nasarawa da Mai Layi da kuma Gidan Kane, inda suka jikkata mutane da dama bayan wadanda suka halaka.
Wasu mazauna yankunan suka ce ‘yan bindigar sun haramta noma a lokacin damina da ke gab da sauka, har sai gwamnati ta janye sojojin da ta girke a wannan yanki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu