Isa ga babban shafi

Yan bindiga sun yi garkuwa da kusan mutane 80 a Zamfara

A karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya sama da mutane 80 ne 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jiya Juma'a.

'Yan sandan Najeriya a jihar Zamfara.
'Yan sandan Najeriya a jihar Zamfara. © REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Mutanen da lamarin ya ritsa da su kamar dai yada rahotanni suka tabbatar daga yankin, bayan isar su daji wajen neman itace da safiyar juma’a,sai labarin sace wasu daga cikin mutanen yankin daga yan bindiga ya kuno kai,a dai dai lokacin da wasu ke cikin aiki a ganakinsu.

Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara mai suna Sani Wanzamai ya ce an yi garkuwa da yara kusan 80 daga kauyen Wanzamai tare da wasu fiye da 20 daga kauyen Kucheri da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar da kuma al’ummar Yankara a makwabciyar Katsina. an kuma sace jihar.

Ana sa ran yawan mutanen da yan bindigar suka yi garkuwa da su tsakanin 80 zuwa 100,yawancinsu matasa ne tsakanin shekarun 15-18 da wadanda suka kai shekaru ashirin. Akwai wani dattijo wanda shekarunsa hamsin ne. Sai dai yawancin wandada aka yi awon gaba da su matasa maza da mata ne.

Ya zuwa wannan lokaci ana dakon sanarwa daga rundunar tsaro domin tabbatar da aukuwar wannan al’amari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.