Isa ga babban shafi

Yan bindiga sun kwashe mazajen wani kauye dake Zamfara

'Yan bindiga a Najeriya sun kwashe daukacin mazajen garin Randa dake karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara saboda bacewar bindigoginsu, yayin da suka yi sanadiyar mutuwar 20 daga cikin su. Rahotanni sun ce mabiya wani gawartaccen ‘dan bindigar yankin da ake kira Lawali Damina ne suka aikata wannan aika aikan na kwashe mazajen wannan gari, cikinsu harda kananan yara saboda bacewar bindigogin mabiyansa guda 2. 

Taswirar jihar Zamfara da ke arewa amso yammacin Najeriya.
Taswirar jihar Zamfara da ke arewa amso yammacin Najeriya. © Wikipedia
Talla

Bayanai sun ce wadannan bindigogi guda biyu sun bace ne lokacin da akayi arangama tsakanin magoyan bayan Damina da wasu abokan gabarsu akan wata budurwa. 

Jaridar Premium Times ta jiyo daga mazauna yankin dake kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Kebbi, inda Yan bindiga ke cin karensu babu babbaka abinda ya faru dangane da kwashe mutanen. 

A wannan yanki ne ‘yan bindiga ke sanya haraji da kuma gindaya sharidodi ga jama’a akan yadda zasu gudanar da harkokinsu na yau da kullum. 

Basaraken Mutumji dake kula da kauyen Randa, Abdulkadir Abdullahi ya shaidawa jaridar cewar tuni kauyen ya biya kudin kariyar da’ yan bindigar suka bukata a karkashin Damina domin kaucewa kai musu hari. 

Bayanai sun ce a makon jiya ne aka fafata tsakanin mabiyan Damina da na abokan adawarsu akan wata budurwa da ta ziyarci yankin daga Shinkafi, abinda ya kaiga kashe wasu daga cikinsu da kuma bacewar makamansu. 

Basaraken yace wannan ne dalilin da ya sa Damina ya ziyarci garin, inda ya bukaci yiwa mabiyansa jana’iza da kuma neman bindigogin da suka mallaka. 

Rahotanni sun ce rashin ganin bindigogin ya sa ya tafi da mutane 270 maza da suka hada da manya da kuma kananan yara. 

Basaraken yace sun shaidawa jami’an gwamnati halin da ake ciki amma babu wanda ya kai musu dauki. 

Ya zuwa wannan lokaci babu wani martani daga gwamnatin jihar Zamfara akan lamarin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.