Isa ga babban shafi

Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa bayan sanya dokar hana fita

Gwamnatin Zamfara da ke Najeriya ta sanar da shirin haramta harkokin siyasa da kuma hana fita na sa’oi 24 a wasu kananan hukumomin jihar sakamakon sake dawowar hare-haren 'yan bindiga.

Gwamnan jihar Zamfara Bello-Matawalle.
Gwamnan jihar Zamfara Bello-Matawalle. © Premiumtimes
Talla

Bayan gudanar da taron majalisar tsaro, gwamnatin jihar ta dakatar da taron siyasar Jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa yau har illa masha Allahu, yayin da ta sanar da sauran Jam’iyyu cewar daga yau an haramta duk wasu tarurrukan da suka shafi siyasa a fadin jihar saboda tabarbarewar tsaro.

Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda jerin hare haren da aka kai wanda ya hallaka jama’a a kananan hukumomin Gusau da Tsafe da Gummi da Bukkuyum da Anka da Bagudu da Maru da Maradun da kuma Kauran Namoda.

Kwamishinan yada labaran Jihar Ibrahim Dosara ya ce taron majalisar tsaron ya dauki matakai masu tsauri domin kare lafiyar jama’a da suka hada da rufe daukacin kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da Gummi, tare da wasu garuruwa da suka hada da Yarkofoji da Birnin Tudu da Rini da Gora Namaye da Janbako da Faru da Kaya da Boko da kuma Madan a sa’oi 24.

Dosara yace an baiwa jami’an tsaro umurnin hukunta duk wani wanda aka samu yana karya dokar hana zirga zirga ko kuma barin gidajen su a wadannan garuruwa.

Kwamishinan ya kuma ce gwamnati ta rufe kasuwannin Danjibga da Bagega, tare da wasu hanyoyin motoci 7 masu muhimmanci domin dakile ayyukan Yan bindigar.

Gwamnati ta bayyana damuwa da halin da jama’a zasu shiga, amma kuma tace daukar matakin ya zama wajibi domin kare lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.