Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda a Zamfara sun karbi miliyan 14 da kwale-kwale a matsayin kudin kariya

Yayin da jami’an tsaron Najeriya ke ci gaba da kai munanan hare haren ta sama da kasa suna samun galaba akan 'yan bindiga da kuma mayakan boko haram, rahotanni daga Jihar Zamfara sun nuna cewar wasu al’ummomin yankin sun gabatar da Naira miliyan 19 da kuma kwale kwale ga 'yan bindigar da ke iko da kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

'Yan ta'addan sun bukaci a biya su fansar ne don baiwa al'ummar yankin damar gudanar da harkokin Noma.
'Yan ta'addan sun bukaci a biya su fansar ne don baiwa al'ummar yankin damar gudanar da harkokin Noma. © Premiumtimes
Talla

Bayanan da ke fitowa daga yankin sun ce mutanen yankunan biyu sun yi gidauniya ne a tsakanin su domin tara wadannan makudan kudade dan bai wa 'yan ta’addan a matsayin kudin da zasu kare su daga hare hare.

Wani dan jaridar da ya fito daga yankin, ya shaidawa Jaridar Premium Times cewar 'yan ta’adda ne suka gindaya sharadin akan mazauna wadannan wurare kafin a fara aikin daminar bana, domin basu damar aiki a gonakin su.

Dan jaridar ya ce mazauna yankin basu da wani abin yi da ya wuce su biya wadannan makudan kudade domin tsira da rayukansu da kuma basu damar noma gonakinsu domin samun abinci.

Mutumin ya bayyana cewar daga cikin garuruwan da suka biya kudin da aka mikawa yan bindigar harda Jargaba da ta bada naira miliyan guda da dubu 600 da Birnin Doki mai naira miliyan guda da Tangaram mai naira miliyan 4, sai kuma Jarkuka mai naira miliyan guda da rabi.

Sauran sun hada da Tuntuja mai naira dubu 500, sai tsafta mai naira miliyan guda da Tudun Magaji mai naira miliyan 2 sai kuma Kadaddaba mai naira dubu 820.

Tudun Kudaku ya biya naira dubu 950, Gargam naira miliyan guda, Kwanar Maje naira dubu 900, Yar Tumali naira miliyan guda, Bawar Daji naira miliyan guda da dubu 700, Tungar Liman naira miliyan 6, sai kuma Makakari mai naira dubu 430.

Shi kuwa garin Yar Sabaya kwale kwale ya sayawa Yan bindigar domin tsallake rafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.