Isa ga babban shafi

Muna son Turji ya tuba a bainal jama'a - Gwmnatin Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta bayyana cewa, ba za ta tabbatar da gaskiyar tubar kasurgumin dan  bindigar nan Bello Turji ba, har sai ya fito ya ajiye makamansa a bainal jama’a.

Bello Turji da yaransa
Bello Turji da yaransa © daily trust
Talla

A ranar Asabar da ta gabata ne, mataimakin gwamnan jihar ya sanar cewa, Turji ya rungumi shirin tattaunawar zaman lafiya, sannan ya yi alwashin fara kadddamar da farmaki kan  sauran ‘yan bindiga a yankin Shinkafi da ke jihar.

A baya dai, gwamnan jihar Bello Matawalle ya bulllo da wani shirin tattaunawar zaman lafiya da ‘yan bindigar a matsayin hanya daya tilo ta kawo karshen hare-harensu da suka dauki tsawon shekaru 10 suna kaddamar wa al’umma tare da sace shanu baya ga garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

An dai samu wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan bindiga da suka mika kansu ga hukuma kamar irinsu Auwalun Daudawa wanda ya kitsa sace daliban makarantar Kankara da ke jihar Katsina a cikin watan Disamban 2020, inda har ya ajiye makamansa a bainal jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.