Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sake sace dalibai a Zamfara

‘Yan ta’adda a Najeriya sun kai hari kan dalibai mata na Kwalejin Lafiya da ke jihar Zamfara inda suka kwashe guda 4 bayan halartar wani bikin aure. 

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Bayanai daga yankin sun ce ‘yan ta’addar sun kama wadannan dalibai ne lokacin da suke komawa Kaura-Namoda daga Birnin Magaji bayan tare motocin da ke dauke da su inda suka kwashi matafiya 18, cikinsu har da daliban mata 4 da wasu ‘yan mata 3 da kuma wani mutum guda. 

Tuni hukumomin Kwalejin Kula da Lafiyar ta hannun shugaban su Yusuf Maradun ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya ce ba’a cikin makarantar aka kwashi daliban ba. 

Maradun ya ce lokacin da aka sace wadannan daliban makarantar na hutun karshen shekara. 

Wani ‘dan uwan daya daga cikin daliban ya ce ‘yan ta’addar sun bukaci diyyar Naira miliyan 20 kafin sakin diyarsu. 

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro musamman hare- hare da kuma garkuwa da jama’a domin karbar kudin fansa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.