Isa ga babban shafi

Zan yi nesa da Abuja bayan rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar idan ya sauka daga karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, zai nesanta kansa da Abuja wajen komawa mahaifarsa ta Daura inda zai ci gaba da rayuwa. 

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari © Bashir Ahmad
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar jakadiyar Birtaniya mai barin gado Catriona Wendy Lang wadda ta je masa ban kwana a fadar shugaban kasar da ke Abuja. 

Buhari wanda ya dade ya na bayyana kagararsa ta komawa gida bayan kwashe kusan shekaru 8 ya na mulkin Najeriya a matsayin zababben shugaban kasa, ya ce ya yi iya bakin kokarinsa kuma lokaci yayi da zai bai wa zababben shugaban kasa damar aiwatar da irin nasa manufofin. 

Shugaban mai barin gado ya taba bayyana cewar dabbobin sa na kewarsa saboda haka zai mayar da hankalinsa wajen kula da su a gonarsa idan ya sauka daga karagar mulki. 

Buhari ya jinjinawa Birtaniya akan hadin kan ta ta ke da Najeriya a bangarori da dama, musamman sake gina yankin Arewa maso Gabas wadda rikicin boko haram ya daidaita. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.