Isa ga babban shafi

Buhari ya amince da dokar tilasta kafa sabuwar gwamnati a kwanaki 60

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a wasu kudirorin da ke yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Julien de Rosa
Talla

Daga cikin kudirorin da ya rattaba hannu a kai, har da wanda zai tilasta wa zababben shugaban kasa da gwmamnoni su mika wa majalisun dokoki sunayen ministoci da kwamishinoninsu a ciki kwanaki 60 daga lokacin da  suka sha rantsuwar kama aiki.

Kudirorin da suka zama doka sun hada da wadanda suka bai wa majalisun dokoki na kasa da na jiha, da bangaren shari’a na jiha damar  cin gashin kai da sauransu.

An tayar da jijiyoyin wuya a shekarar 2015, lokakcin da shugaba Buhari ya shafe watanni 6 kakfin ya nada ministocinsa.

A ranar Larabar da ta gabata,  zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu  ya yi bayani a kan irin mutanen da zai nada a matsayin ministocinsa, inda ya ce zai nada wadanda suka san makaman aiki ne daga ko ina suke a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.