Isa ga babban shafi

Najeriya ta samu sabbin wadanda suka kamu da covid-19 5 a jihohi 2

Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC a Najeriya ta sanar da samun akalla mutane 5 da suka harbu da cutar corona a sassan kasar daga ranar 25 ga watan Fabarairu zuwa 31 ga watan Maris din da ya gabata.

Tun bayan wadatuwar rigakafin cutar Najeriya ke ganin saukar alkaluman masu harbuwa da Covid-19 a sassan kasar.
Tun bayan wadatuwar rigakafin cutar Najeriya ke ganin saukar alkaluman masu harbuwa da Covid-19 a sassan kasar. © capture d'écran/lemonde.fr/afrique
Talla

Alkaluman da hukumar ta fitar a yau asabar sun nuna cewa sabbin kamuwa da cutar sun fito ne daga jihohin Lagos da Rivers wadanda kuma tuni aka killace su don dakile yaduwar cutar.

NCDC ta bayyana cewa mutum 4 suka harbu da cutar a jihar Lagos yayinda wani 1 ya harbu da ita a Rivers, lamarin da ke sanya fargabar yiwuwar dawowa da kuma fantsamuwar cutar a sassan Najeriya.

Zuwa yanzu alkaluman NCDC na nuna cewa mutum dubu 266 da 665 suka harbu da cutar Covid-19 a Najeriyar tun daga lokacin da aka samu bullar cutar zuwa yanzu.

A cewar NCDC cikin jumullar wadanda suka kamu da cutar covid-19 a Najeriya mutum subu 259 da 951 sun samu warkewa yayinda cutar ta kashe mutum dubu 3 da 155 a jihohin kasar 36 da birnin Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.