Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Najeriya ta samu karin masu korona 681, adadi mafi girma a rana 1

Da'alam dai tsugune bai kare ba dangane da annobar Korona a Najeriya, bayan da kasar ta sanar da samun sabbin mutane 681 da suka kamu da cutar a kasa da sa'o'i 24 wato daga jiya Alhamis kenan, adadi mafi yawa da Najeriyan ta taba samu tun bayan bullarta a kasar, duk da cewa fargabar da ake da ita a sakanin al'umma ya ragu ainun, abangare guda suma mahukunta sun sake mara don gudanar da harkokin yau da kullum. 

Wani da akewa gwajin cutar COVID - 19 a Maiduguri a Najeriya
Wani da akewa gwajin cutar COVID - 19 a Maiduguri a Najeriya Audu Marte/AFP/Getty
Talla

Wannan sabon adadi dai ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 14,554, a Najeriyar, yayin da 387 suka mutu.

Sabbin alkaluman da Hukumar yaki da cututtuka ta bayar sun ce an samu mutane 345 a Lagos, wato kussan rabin adadin da aka samu na fadin kasar kenan a rana guda.

Jihar Rivers ce ta biyu a yawan wadanda suka kamu, inda ta ke da mutum 51, sai Ogun mai mutum 48 da suka kamu, Gombe na da  47 da suka kamu, sai Oyo mai mutane 36, Imo 31, Delta 28, Kano 23, Bauchi 18 sai Edo mai mutum 12, Katsina ma na da 12.

Sauran jihohin Najeriyar da aka samu sabbin wadanda suka kamu ranar Alhamis, sun hada da Kaduna mai da mutane 9, sai Anambra 7, Jigawa 5, Kebbi da Ondo hur-hudu, sai kuma Nasarawa mai mutum guda.

A wannan karon ba a samu ko da mutun daya da ya kamu da cutar coronavirus a babban birnin tarayya Abuja.

 

 

 

 

 

ji

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.