Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Za a cigaba da gwajin hydroxychloroquine kan cutar coronavirus a Najeriya - NAFDAC

Hukumar tantance ingancin magunguna da kayayyakin abinci ta Najeriya NAFDAC, tace gwajin maganin Hydroxy-chloroquine don warkar da masu cutar coronavirus zai cigaba da gudana, duk da cewa hukumar WHO ta dauki matakin dakatarwar wucin gadi kan nazarin da take yiwa maganin.

Kwayoyin maganin Hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin malaria.
Kwayoyin maganin Hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin malaria. AFP
Talla

Sanarwar hukumar NAFDAC, na zuwa ne sa’o’i bayan da a ranar Litinin hukumar lafiya ta duniya WHO, ta dakatar da gwajin maganin Hydroxy-chloroquine kan masu cutar coronavirus domin warkar dasu, saboda matsalar da wasu masana suka ce maganin na tattare da shi.

Hukumar ta WHO ta ce matakin nata ya biyo bayan binciken masanan da mujallar Lancet ta wallafa dake cewar maganin na Chloroquine na kara tsawaita sabubban mutuwar masu cutar coronavirus ne, a maimakon ceto rayuwarsu.

Sai dai shugabar hukumar tantance ingancin magunguna ta Najeriya Mojisola Adeyeye, ta ce bayanan da kwararru suka tattara a kasar ya nuna cewar, maganin na Hydroxy-chloroquine na tasiri matuka wajen warkar da wadanda suka kamu da cutar coronavirus.

Adeyeye ta ce mafi akasarin masu cutar da suka warke an yi amfani da Chloroquine ne a matsayin mafi rinjayen magungunan da aka basu, sai dai maganin yafi tasiri kan wadanda cutar ta coronavirus ba ta yiwa mugun kamu ba.

Har yanzu dai ana cigaba da tafka muhawara tsakanin masana kimiyya da lafiya dangane da amfani da maganin na Chloroquine ko Hydroxy-chloroquine don warkar da masu cutar coronavirus, inda wasu ke nuna shakku a kansa ciki harda ministan Lafiyar Faransa Olivier Veren a baya bayan nan, yayinda ita kuma cibiyar binciken magungunan India ta bada umarnin rugumar maganin, bayan tabbatar da tasirinsa wajen warkar da cutar coronavirus.

Shi ma dai a nasa bangaren shugaban Amurka Donald Trump, ya fito karara a makon jiya, inda ya bayyana wa duniya cewa, lallai yana kwankwadar wannan magani, a bin da ya sa a yanzu kasashen duniya ke ta rige-rigen sayen adadi mai yawa na maganin.

Shi ma Ministan Lafiyar Brazil, ya ce, hydroxy-chloroquine gami da maganin cutar Malaria, na magance cutar COVID-19, amma ga wadanda ba ta tsanata ba a jikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.