Isa ga babban shafi

Mayakan ISWAP sun kashe 'yan Boko Haram 200

Mayakan Kungiyar ISWAP sun halaka mayakan Boko Haram sama da 200, bayan wani sabon fada da ya barke tsakaninsu a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan Boko Haram AFP FOTO / BOKO HARAM
Talla

Wannan ya nuna yadda wutar gaba ke ci gaba da ruruwa tsakanin bangarorin biyu masu ikirarin jihadi.

Tuni mazauna yankin suka bayyana wa RFI Hausa irin murnar da ta lullube su saboda yadda mayakan ke kashe junansu.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu Bilyaminu Yusuf cewa, babu shakka addu'ar bayi-Allah ce ke aiki a kan wadannan mayakan da suka hana jama'a sakat.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Bilyaminu Yusuf daga birnin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.