Isa ga babban shafi

Jam'iyyun adawa a Najeriya sun bukaci a sake sabon zabe

A Najeriya, gamayyar jam'iyyun siyasa uku PDP, Labour Party (LP) da kuma African Democratic Party (ADC) sun kada kuri'ar rashin amincewa da Mahmoud Yakubu, a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC, inda suka bukaci ya gaggauta yin murabus. daga mukaminsa.

'Yan takarar jam'iyyun LP, PDP, da kuma ADC
'Yan takarar jam'iyyun LP, PDP, da kuma ADC © dailytrust
Talla

Gamayyar kungiyoyin sun yi kira ga gwamnati da ta soke zaben baki daya da aka gudanar ya zuwa yanzu, saboda yawaitar matsalolin da suka dabaibaye zaben.

A yayin da kungiyar ta roki shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta shiga tsakani don ceto dimokuradiyya ta hanyar nada mutum mai gaskiya don kammala babban zaben 2023, kungiyar ta yi nuni da cewa irin wannan tsarin zai taimaka wajen karfafa sha’anin siyasar Najeriya, musamman wajen gudanar da sahihin zabe.

Kungiyar ta yi nuni da cewa magudi ya yi yawa, shi ya sa ta barranta kanta daga zaben, domin sanar wa ‘yan Najeriya da sauran al’ummar duniya halin da ake ciki.

Kungiyar yayin da ta kuma bayyana cewa har yanzu ana kan tattara sakamakon zaben da kuma kai su gidajen gwamnati domin a yi amfani da su, ta kara da cewa “ba za a iya gyara tsarin ba saboda keta doka da ake yi.

“Tunda sun gaza, ba za a iya gyara tsarin ba saboda ba za su iya gyara barnar da aka yi a zaben ba, abu ne da ba za a iya dawo da shi ba kuma ya kamata a sake gudanar da sabon zabe.

“Don haka ne muke kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nada sabon shugaban hukumar zabe ta INEC, sannan ya kamata ya dawo hayyacinsa kuma ya gaggauta daukar matakin da ya dace, domin ba ma son jama’ar mu su fito kan titi, suna daukar doka a hannu,” in ji kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.