Isa ga babban shafi

An hana tsohon mai baiwa shugaba Buhari shawara ganawa da Tinubu

Ita Enang, tsohon mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, jami'an tsaro sun hana shi samun damar ganawa da Bola Tinubu a lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ziyarci jihar Akwa Ibom a yakin neman zabensa.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari da dan takarar jam'iyyar APC  Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da dan takarar jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu © Nigeria Presidency
Talla

Bola Tinubu ya je Uyo ne a ranar 30 ga watan Janairu domin ci gaba da rangadin yakin neman zabensa a fadin kasar gabanin zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ita Enang, wanda dan takarar gwamna ne na jam’iyyar a shekarar 2023 a Akwa Ibom, ya kasance a filin jirgin sama na Victor Attah, Uyo, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da dama, wajen tarbar dan takara Bola Tinubu, amma jami’an tsaro suka ware su suka ce masa ba zai je ba.

Jam’iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom, kwanaki kadan gabanin ziyarar Bola Tinubu, ta sanar da korar Ita Enang daga jam’iyyar APC saboda karar da ya ke yi kan tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a jihar. Sai dai Ita Enang ya kore su, yana mai kiran kan sa da zama dan jam’iyyar.

Ita Enang ya tabbatar wa manema labarai cewa an hana shi ganawa da Bola Tinubu a filin jirgin sama da ke Uyo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.