Isa ga babban shafi
Zaben Najeriya

Kiristocin APC sun fusata kan hada Tinubu da Shettima

Wasu jiga-jigan ‘yan siyasa mabiya addinin Kirista kuma mambobi a Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, sun yi watsi da matakin da jam’iyyar ta dauka na tsayar da Kashim Shettima a matsayin mataimakin Bola Ahmed Tinubu a zaben shugabancin kasar mai tafe.

Bola Ahmed Tinubu tare da Kashim Shettima
Bola Ahmed Tinubu tare da Kashim Shettima © Premiumtimes
Talla

Tinubu da Shettima dukkaninsu Musulmai ne, abin da ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar da sauran al’ummar kasar, inda wasu ke ra'ayin cewa, hakan kuskure ne.

Manyan mambonin na APC mabiya addinin Kiristan sun bayyana matakin na hada Musulmi da Musulmi a matsayin rashin hankali, duba da irin cakuduwar da ake da ita a Najeriya ta Musulmai da Kiristoci da sauran mabanbantan kabilu.

Kazalika sun ce, wannan tsarin tamkar yaudara ce ga fafutukar hada kan kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Sun dai sanar da matsayarsu ce bayan wani taro da suka gudanar a jiya Talata a birnin Abuja tare da fitar da wata sanarwa dauke da sa-hannun Farfesa Doknan Sheni.

Mambobin na APC sun ce, babu yadda za su iya shawo kan al’ummominsu da ke mazabarsu don ganin sun zabi Musulmi da Musulmi a yayin zaben shugabancin kasar na 2023.

Har ila yau, jiga-jigan na APC sun zargi jam’iyyar APC da yin watsi da bukatun Kiristocin duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban Jam’iyyar a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.