Isa ga babban shafi

Najeriya: Kotu ta ce dan takarar APC ne ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

Kotun sauraron shari’ar zabe a Najeriya ta yanke hukuncin soke zaben gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP, inda ta bayyana tsohon gwamna Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a bara. 

Ademola Adeleke lokacin da aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Osun
Ademola Adeleke lokacin da aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Osun © Ademola Adeleke
Talla

Shugaban kwamitin alkalan da suka saurari karar Terste Kume ya karanta hukuncin kotun yau a birnin Oshogbo, inda ya bada umurni ga hukumar zabe da ta karbe takardar samun nasarar zaben da aka baiwa Adeleke domin mikawa Oyetola. 

Mai shari’a Kume yace sun gamsu cewar hukumar zaben Najeriya ta gudanar da zaben kamar yadda dokar zabe ta tanada, saidai an samu kuri’un da suka wuce kima a wasu mazabu, abinda ya sa aka janye alkaluman da ake tababa akai. 

Kume yace bayan janye wadancan haramtattun kuri’u sakamakon zaben ya nuna cewar Oyetola ya lashe zaben da akayi da kuri’a 314,921, saboda haka ta bada umurnin rantsar da shi a matsayin wanda ya samu nasara.  

Bayanai sun ce daga cikin alkalai 3 da suka saurari karar, 2 sun goyi bayan soke zaben Adeleke, yayin da guda yaki amincewa. 

‘Yan takara 15 suka shiga takarar zaben gwamnan Osun da akayi bara, wanda hukumar zabe ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya samu nasara, abinda ya sa Oyetola rugawa kotu domin gabatar da korafinsa dangane da zaben, yayin da ya gabatar da zargin kada kuri’un da suka wuce kima a wasu mazabu dan bi masa hakkinsa. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.