Isa ga babban shafi

APC a Adamawa za ta daukaka kara kan hana ta tsayar da dan takarar gwamna

Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa a jiya asabar ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke na dakatar da ita daga tsayar da dan takarar gwamna a zaben 2023 a jihar.

Aishatu Binani yar takarar Gwamna a APC
Aishatu Binani yar takarar Gwamna a APC © daily trust
Talla

Wata babbar kotun tarayya da ke Yola, a ranar Juma’a da ta gabata, ta soke zaben fidda gwani na jam’iyya mai mulki APC a wannan jihar.

Jam’iyyar ta zabi Aishatu Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar a zaben fidda gwanin da aka soke a ranar 26 ga watan Mayu na wannan shekara. Ta samu kuri’u 430 inda ta doke abokin hamayyarta Nuhu Ribadu wanda ya samu kuri’u 288.

Alkalin kotun, Abdulaziz Anka, ya kuma ki amincewa da rokon da jam’iyyar ta yi na sake gudanar da sabon zaben fidda gwani, wanda hakan ke nufin jam’iyyar ba za ta samu dan takara a zaben ba.

Nuhu Ribadu dai ya garzaya kotu ne bisa zargin rashin bin ka’ida wajen gudanar da zaben fidda gwani.

Kotun ta ce zaben fidda gwanin bai bi ka’idar zaben 2022 ba, da kundin tsarin mulkin Najeriya, da ka’idojin jam’iyya.

Alkalin ya ce nadin na uwargida Binani ya sabawa sashe na 85 na dokar zabe saboda an yi tazarce a lokacin zaben fidda gwani.

Da yake magana a wani taron manema labarai a  jiya ranar asabar, sakataren jam’iyyar APC na jihar, Raymond Chidama, ya roki magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankalinsu, ya ce jam’iyyar za ta daukaka kara kan hukuncin.

Ya ce bayan yanke hukuncin ne shugabannin jam’iyyar na jihar suka yi taro inda suka amince su dawo da aikinsu ta hanyar kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.