Isa ga babban shafi

APC ta dage ranar kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar APC ya sanar da dage fara gudanar da yakin neman zaben, wanda a baya ya tsayar da gobe laraba a matsayin ranar da za a dasa harsashin fara gangamin yakin neman zaben na shekarar 2023.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Tinubu lokacin da ya ke daga hannun kashim Shettima a matsayin wanda za su yi takara tare.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Tinubu lokacin da ya ke daga hannun kashim Shettima a matsayin wanda za su yi takara tare. © Kashim Shettima
Talla

Wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC ya fitar karkashin jagorancin gwamnan jihar Pulato Simon Lalong a yau talata ya ce daukar matakin na da nasaba da rashin wadatattun masu ruwa da tsaki a tafiyar.

A cewar sanarwar kwamitin ya ba shi da damar kara fadada kwamitin yakin neman zaben don kara sanya masu ruwa da tsaki a ciki.

Simon Lalong ya ce nan bada jimawa ba za a sanar da sabuwar ranar da za su kaddamar da yakin neman zaben.

Ko a daren Lahadi sai da kwamitin ya fidda sanarwar dage rantsar da mambobin kwamitin daya tsara gudanarwa a jiya litinin zuwa gobe laraba gabanin sanarwar ta yau talata da ke nuna babu takamaiman ranar rantsarwar da za ta bayar da damar fara yakin neman zaben.

Duk da ya ke akwai rade-radin da ake yi cewar wasu gwamnonin jam’iyar basu gamsu da jerin wadanda aka sanya a cikin kwamitin ba, rahotanni na nuna cewar wannan dage kaddamar da fara yakin neman zaben ba shi da alaka da hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.