Isa ga babban shafi

Nigeria: Yau APC ke taron fitar da gwani na neman takarar shugabancin kasa

Yayin da yau Litinin 06 ga watan Yunin 2022, Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke shirin gudanar da taron ta na kasa domin gudanar da zaben fidda gwani wanda zai bata damar gabatar da ‘dan takarar zaben shekara mai zuwa, rahotanni sun ce har ya zuwa safiyar wannan Litinin yunkurin shugabannin Kudu maso yamma ko kuma bangaren Yarbawa na sasanta masu bukatar yin takarar domin gabatar da mutum guda ya faskara.

Mataimakin Shugaban kasan Najeriya Yemi Osinbajo da Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila.
Mataimakin Shugaban kasan Najeriya Yemi Osinbajo da Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila. © LAGOS STATE
Talla

Tun daga daren Asabar da Gwamnonin APC guda 9 dake mulki a yankin arewacin Najeriya suka bayyana matsayin su na baiwa kuduncin kasar damar fitar da ‘dan takara, shugabannin Yarbawa suka fara gudanar da taruka tare da masu sha’awar takarar domin sasanta su amma har yanzu babu abinda ya sauya.

'Yan takara sun kasa fahimtar juna

Taron wanda ke gudana a karkashin jagorancin shugaban APC na farko Bisi Akande tare da Gwamnonin da suka fito daga yankin da kuma ‘Yan takarar ya gaza dinke barakar dake tsakanin masu bukatar tsayawa takarar da suka hada da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da Tunde Bakare da Ibikunle Amosun da Dimeji Bankole.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘Yan takarar da su hada kai wajen gabatar da ‘dan takara guda daya tilo da za’a gabatar a zaben fidda gwanin ba tare da samun rarrabuwar kawuna ba, amma bisa dukkan alamu kowanne ‘dan takara ya dage shi yafi dacewa ya yiwa jam’iyyar takara.

Tinubu ko Osibajo

Rahotanni daga tarurrukan da ake yi na sasantawar da zummar fitar da ’dan takara guda na nuna cewar ana samun mahawara mai zafi tsakanin bangaren jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da kuma na mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, inda kowanne bangare ke tauna tsakuwa da kuma kekashe kasa cewar ba zai hakura ba.

Kafin dai wannan lokaci, magoya bayan manyan Yan takarar guda biyu sun fara musayar kalamu masu zafi da batunci a tsakanin su inda suke zargin juna da cin amana da kuma neman zagon kasa ga bukatar Yankin Kudu maso yamma na samun kujerar shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Daraktan yakin neman zaben Bola Tinubu kuma tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima yace babu wanda ya isa ya sa gwanin sa ya sauka daga takarar neman tikitin APCn yayin da suka bayyana aniyar su ta samun nasara muddin za’a gudanar da zaben fidda gwani ba tare da magudi ba.

Kashim ya bada hakuri

Tsohon gwamnan Jihar Bornon, Sanata Kashim Shettima, ya nemi afuwar Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Ahmad Lawan shugaban Majalisar dattawa bisa kalaman muzantawa da ya yi a kansu.

A ranar Alhamis da ta gabata ne kashim Shettima ya bayyana cewa Farfesa Osinbajo mutumin kirki ne, "amma mutanen kirki ba su dace da shugabanci ba sai sayar da gurgugu da Ice Cream.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.