Isa ga babban shafi

Ministocin Najeriya 10 sun yi murabus domin tsayawa takara a zaben 2023

Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce zuwa Juma’ar da ta gabata, ministoci 9 suka sauka daga mukamansu bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya umarci su yi hakan kafin ranar 16 ga wannan wata na Mayu, bayan da suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takara a zabuka masu zuwa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Bayanai sun ce a ranar Juma’a shugaban Najeriyar ya gana da dukkanin ministocin da suka ajiye ayyukansu nasu a Abuja, inda ya yi musu bankwana gami da fatan alheri dangane da aniyar da suka sanya a gaba.

A baya bayan nan Ministan kwadago da samar da ayyukan yin a Najeriya, Sanata Chris Ngige, ya sanar da janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a jiya Juma’a, inda ya yi alkawarin kauracewa shiga al’amuran siyasar jam’iyyarsa ta APC mai mulki.

Rahotanni sun kara da cewar tuni shi ma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya janye daga takarar neman kujerar Gwamnan jihar Kebbi domin maye gurbin Atiku Bagudu.

Bayan shafe watanni ana cece-kuce kan rade-radin shiga takararsa ce, Ministan shari’ar ya shiga jerin masu neman kujerar gwamnan jiharsa ta Kebbi a watan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.