Isa ga babban shafi

Buhari ya baiwa Ministoci masu son shiga zabe umarnin ajiye mukamansu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa ministocin sa dake bukatar tsayawa takarar zabe da su aje mukaman su nan da ranar 16 ga watan nan kamar yadda doka ta tanada.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed, yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja.
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed, yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yanzu haka akalla ministoci 10 suka sayi fom din takarar shugaban kasa da gwamna da kuma majalisun tarayya, cikin su har da Rotimi Amaechi da Abubakar Malami da Pauline Tallen

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya yi Karin haske akan umurnin, inda ya ce, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne kawai wanda umarnin bai shafa ba, a matsayinsa na zababben da jama’a suka kadawa kuri’a.

01:03

MInistan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.