Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe-Buhari

Buhari ya umarci gwamnan CBN ya sauka daga mukaminsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci gwamnan babban bankin kasar CBN Godwin Emifiele ya sauka daga mukaminsa sakamakon bayyana aniyarsa ta shirin tsayawa takara a zaben 2023.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da gwamnan babban bankin kasar CBN Godwin Emefiele.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da gwamnan babban bankin kasar CBN Godwin Emefiele. Daily Trsut
Talla

Rahotanni sun bayyana yadda sakataren gwamnatin Najeriyar Boss Mustapha ya mika bukatar hakan ga daukacin mukarraban gwamnati da ministocin da ke shirin tsayawa takara ciki har da Emifiele.

Wasikar shugaba Buharin na dauke da rubutun cewa wajibi ne ministoci, shugabannin hukumomi da jakadu baya ga masu rike da mukaman siyasa su gaggauta sauka daga kujerunsu kafin nan da ranar 16 ga watan da muke ciki na mayu.

Emefiele ya shiga tsaka mai wuya ne sakamakon caccakar da ta yi masa yawa tun bayan da hadakar wasu kungiyoyi suka tattara kudi tare da saya masa fom din takarar neman kujerar shugabancin Najeriya a zaben 2023 karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu da ke sahun ‘yan gaba gaba a masu caccakar Emefiele ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke gwamnan babban bankin da karfi matukar ya ki amincewa da sauka daga kujerarsa kamar yadda aka bukata.

A bangare guda babbar jam’iyyar adawa a Najeriyar PDP ta bukaci daure Emefiele wanda ta ce bayyana aniyar tasa ta tsayawa takara a zaben na 2023 ya sabawa doka.

Tuni dai ministoci 3 daga cikin 9 da suka bayyana aniyar tsayawa takarar suka sanar da ajje mukamansu tun a jiya laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.