Isa ga babban shafi

Zaben 2023: Ko wanene zai lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar APC?

An soma gwajin-kwanji gabanin zaben fidda gwani tsakanin mutane 23 da ke neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, wadanda nan da ‘yan kwanaki za su san makomarsu.

Mambobin majalisar gudanarwar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Mambobin majalisar gudanarwar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. © Femi Adesina
Talla

Akwai wakilai ko kuma deliget har guda 7 da 800 da za su wakilci daukacin magoya bayan jam’iyyar APC wajen zaben mutumin da suke ganin ya fi cancantar lashe tikitin tsayawaa takarar a zaben na 2023.

Jagoran APC kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na cikin na gaba-gaba a jerin wadanda ake sa ran za su iya lashe tikitin takarar  shugaban kasar, ganin yadda kowanne daga cikin manyan ‘yan siyasar biyu ke da tasiri sosai.

Osinbanjo ya yi biris da uban gidansa

Duk da cewa, Tinubu ne uban-gidan Osinbajo a siyasance, mataimakin shugaban kasar ya yi biris, inda ya bayyana aniyarsa ta yin fito-na-fito da mai-gidansa, lamarin da ya haifar da ‘yar tsama a tsakaninsu.

Wannan ne ya sa ake ganin cewa, lallai za a kwashi kallo a tsakanin jagororin biyu da suka fito daga yanki da kuma kabila guda.

Sauran fitattun ‘yan takarar sun hada da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan da Rotimi Amaechi da Godswill Akpabio da Rochas Okorocha da Ibikunle Amosun da Ben Ayade da Tunde Bakare da Kayode Fayemi da Ken Nnamani.

Sai kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello da gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar da Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura da Dimeji Bankole.

Kasuwar Wakilan Jam'iyya ta kankama

Gabanin wannan zaben, an ga yadda masu neman tikitin suka yi ta kara-kaina tsakanin jihohin Najeriya da zummar zawarcin kuri’un wakilan, inda har wasu rahotanni ke cewa, masu neman takarar sun yi yayyafin kudi da wasu nau’uka na kyautuka don saye kuri’un daga hannun deliget din kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito a makon jiya.

Sai dai a cewar Jaridar, ta zanta da wasu daga cikin wakilan kuma sun tabbatar mata da cewa, duk da gudunwamar kyautar da aka ba su, hakan ba zai hana su zaben mutumin da ya fi cancanta ba, lamarin da lallai ‘yan kasar za su yi na’am da shi muddin wakilan suka tabbata akan wannan kudiri nasu na yin watsi da son zuciya.

Watakila wadannan deliget za su yi taka-tsan-tsan ne wajen zabo dan takara mafi dacewa, domin ganin jam’iyyarsu ta APC ta kai labari a zaben mai tafe, in ba haka ba, babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta iya yi musu fintikau a babban zaben na shugaban kasa muddin ta yi dabarar tsayar da dan takarar da ‘yan Najeriya suka yaba da nagartarsa.

A halin da ake ciki ana iya cewa, babu shakka lokaci ya yi da ya kamata a ajiye akidar banbance-banbance na kabilanci ko yanki ko kuma addini domin zaben mutumin da ya fi dacewa wanda kuma ke da kwarewa wajen tunkarar matsalolin  Najeriya da suka yi mata dabaibayi musamman ma matsalar tsaro da rugujewar tattalin arziki.

Hakki mai nauyi ya rataya a wuyan Wakilan Jam'iyya

Masu zaben  fidda da gwani dai na taka muhimmiyar ruwa wajen kare mutunci ko kuma cin mutuncin demokuradiya a Najeriya, inda aka sha kokawa da su saboda yadda suke karbar na goro daga masu neman tikitin tsayawa takarar, abin da ya sa ake cewa, iya zurfin aljihunka, iya yawan kuri’un da za su zuba maka.

Wasu rahotannin bayan-fage na cewa, Jam’iyyar APC na fatan samun hadin kai tsakanin mambobinta domin cimma jituwa ta bai-daya dangane da mara baya ga mutun daya tal tsakanin masu neman tikitin, a maimakon a dauki lokaci wajen fafatawa tsakanin mutane 23 da kowannensu ke son maye kujerar shugaba Muhammadu Buhari.

Tun da farko dai, babu wanda ya zaci cewa, adadin masu neman tsaya wa APC takara zai kai 23, inda kowanne daga cikinsu ya lale zunzurutun Naira miliyan 100 domin sayen fom, lamarin day a  haddasa cece-kuce daga ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.