Isa ga babban shafi
Najeriya

Tinubu ya bayyana aniyar tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya

Jagoran jam’iyyar APC a Tarayyar Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya kawo karshen rade-raden da ake yi dangane da sha’awarsa ta tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu Nigeria Presidency/Handout via Reuters
Talla

Tinubu ya yi wa magoya bayansa bushara ne, yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja, bayan ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Tinubu ya bayyana cewa ya shaidawa shugaban kasar aniyarsa ta shiga jerin masu neman maye gurbinsa idan wa’adinsa na biyu ya cika a shekarar 2023.

Koda yake an dade da ganin alamun tsohon gwamnan na Legas na fatan darewa kujerar shugabancin Najeriya, Tinubu ya dade yana kaucewa yin magana akan al’amarin, abinda ya haifar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeriya akan hasashen da ake yi akan bukatar tasa da kuma irin salon mulkin da zai jagoranta, idan har burin na sa ya cika.

A watan Oktoban shekarar bara, Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya bi sahun sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar wajen kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Tinubu a 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.