Isa ga babban shafi

APC ta sauya lokacin zaben fitar da gwanin takarar shugaban kasa

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta dage gudanar da zaben fidda gwanin da zai tsaya mata takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023, daga ranar 29 ga watan Mayu, zuwa 6 ga watan Yuni.

Sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu.
Sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu. © Daily Trust
Talla

Sakataren watsa labaran jam’iyyar ta APC na kasa, Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar sa’o’i bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta karawa jam’iyyu wa’adin lokutan da ta tsayar musu domin su gudanar da zaben fitar da gwani.

A jiya Juma’a ne dai hukumar INEC ta sanar da tsawaita wa'adin da ta baiwa jam'iyyun siyasar Najeriya na zabukan fidda gwani da adadin kwanaki shida.

Da farko dai wa’adin ranar 3 ga watan Yuni hukumar ta sanar, amma a yanzu ta maida shi zuwa tsakanin 4 da 9 ga watan na Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.