Isa ga babban shafi

Babu abin da zai hana gudanar da zabe a Najeriya- Gwamnati

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa da al’ummar kasar cewa babu abin da zai hana gudanar da babban zaben kasar da ke tafe a watannin Fabariru da Maris din shekarar da muke ciki ta 2023 duk da barazanar tsaron da kasar ke fuskanta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Bashir Ahmad
Talla

Minstan yada labarai na Najeriyar, Lai Mohammed wanda ya bayyana haka a Abuja, ya ce gwamnati ba ta sauka daga kudirinta na gudanar da zabe kamar yadda aka tsara ba.

Kalaman gwamnatin dai na zuwa ne bayan hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta yi kashedi cewa idan har ba a shawo kan matsalar tsaron da wasu sassan kasar ke fama da shi ba, babban zaben kasar na iya faskara.

A cewar INEC ko da an iya gudanar da zaben a wasu sassan alamu na nuna cewa babu tabbacin iya gudanar da su a wasu sassa saboda matsalar ta tsaro, lamarin da tuni ya haddasa cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya.

Haka zalika tuni, masana tsaro suka fara nuna yatsa ga hukumar ta INEC wadda suka ce bata da hurumin sanar da wannan mataki a radin kanta har sai ta tuntubi bangarorin tsaron kasar.

Najeriya dai na fama da jerin matsalolin tsaron da suka kunshi 'yan ta'adda da ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a yankin arewa maso gabashin kasar baya ga 'yan bindiga da ke satar mutane da kuma kashewa don neman fansa a yankin arewa maso yammaci.

Kauyuka da dama ne musamman a jihohin Zamfara da Sokoto da kuma Neja yanzu haka ke karkashin ikon 'yan bindigar wadanda ke sanya musu haraji gabanin samun damar yin warkajami ko kuma gudanar da sana'o'insu koma noma a yankunan na su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.