Isa ga babban shafi

Gwamnatin Kano tayi amai ta tande dangane da hana Adaidaita Sahu aiki

Gwamnatin Jihar Kano dake Najeriya ta dakatar da shirin haramtawa masu haya da kekunan Adaidata Sahu kwana guda bayan fara amfani da dokar wadda ta haifar da matsalolin sufuri da kuma zirga zirgar jama’a a birnin Kano. 

Gwamnatin Kano ta haramta zirga-zirgar Adaidaita Sahu
Gwamnatin Kano ta haramta zirga-zirgar Adaidaita Sahu © LegitHausa
Talla

Shugaban Hukumar KAROTA, wato Hukumar dake kula da harkokin sufuri na Jihar, Baffa Dan-Agundi ne ya sanar da sauyin matsayin, saboda abin da ya kira korafe korafen da jama’a suka gabatar. 

Dan Agundi yace gwamnati ta saurari korafe korafen jama’a saboda haka ta amince da bukatar shugabannin kungiyar masu hayar Adaidaita sahun saboda irin matakan da suka dauka na gabatar da kokensu cikin dattako. 

Shugaban Hukumar ya bukaci masu kekunan da su koma bakin aiki a manyan titunan birnin, yayin da suma sabbin motocin da gwamnati ta gabatar zasu ci gaba da nasu ayyukan. 

Wakilin RFI Hausa da ya zagaya sassan birnin Kano yau ya ga tarin matafiya da suka hada da yan kasuwa da ma’aikata da kuma dalibai ba tare da motocin da zasu kaisu inda zasu ba. 

Kano ne birni mafi girma a yankin arewacin Najeriya wanda ke tara yan kasuwa daga sassa daban daban na kasashen Afirka dake gudanar da harkokin yau da kullum. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.